Yadda Ake Sa Wayar “CHINA PHONE” Ta Dinga Shiga Intanet Da Layukan Najeriya



A yanzu kana iya sa wayarka da ake kira “China Phone” ta yi maka browsing ta hanyar amfani da kowanne ɗaya daga cikin layukan sadarwa na Nijeriya wato MTN, GLO, AIRTEL, ko kuma ETISALAT. Nigeria tafi fice a cikin ƙasashen dake amfani da wayoyin salula ƙirar China. Kana iya cewa ma mafi yawan kayayyakin da ake amfani da su ƙirar China a wannan ƙasar tamu babu kamar wayar hannu ta salula. Sauƙin su da kuma samun a kowanne saƙo da lungunan kasuwanni ya sa suka samu karɓuwa A yawan lokaci mafi akasarin mutane na son sayan wayoyi ƙirar China ne saboda kyawunsu da daɗin ko sauƙin sha’anin su. Hakan ya sa ma har suke iya gogayya da sauran kamfononin waya kamar su Nokia, Samsung, LG da dai sauransu. Kai hatta wayoyin dake da ake kira da komai da ruwanki (smart phone) kamar su Blackberry, iphones da kuma Andriod su kansu ba ƙaramin gogayya suke fuskanta ba daga wayoyi ƙirar China. Kamar yadda aka sani ne cikin kowane da daɗi akwai rashin sa. Domin wani abin takaici da waɗannan wayoyin shi ne yadda kamfononin sadarwan mu ba sa iya turo maka da tsarin shiga intanet’ (Automatic Settings) kai tsaye kamar yadda suke turo wa wayoyi saɓaninsu. Duk wayar da ba ta da GPRS to fa ba ta iya shiga Intanet, domin ba ka da damar kaima ka iya yin bincike da kuma ninƙaya a sarari na Intanet. Shiga cikin irin wannan matsalar ya sa ni bincike har na gano yadda ake iya canza wannan tsarin: 1. Shiga “menu” sannan ka hau” Service/Intanet access” 2. Ka taɓa “service/Intanet Access” sannan ka zaɓi “wap Browser” 3. Buɗe ‘Wap browser’ sai kuma ka shiga “settings” 4. Buɗe “Edit profile” sai ka zaɓi wanda kake so 5. Zaɓi “Edit profile” sai ka shigar da ɗaya daga cikin bayanan da za mu jero a ƙasa wanda ya yi daidai da layin wayarka. Homepage: MTN: GLO: AIRTEL: Wap.ng.airtel.com@ ETISALAT: Wap.etisalat.com.ng@ 6. Sai ka shiga “Data Account” ka zaɓi wanda kake so misali China Mobile GPRS 7. Wajen da ake rubuta “Connection type” sai ka rubuta “WAP 8. WAJEN “Proxy/IP Address sai ka zaɓi irin layinka ka rubuta waɗannan lambobi kamar haka: MTN: 010.199.212.002 AIRTEL: 072.018.254.002 GLO: 190.129.010.245 ETISALAT: 072.055.142.251 9. Sai wajen da aka rubuta “Security” sai ka sa “off” 10. Username: Wap. Password: Wap (idan ka gama sai ka danna “yes” sannan kai amfani da hanyar fita ta baya “back button”) ka fita. 11. Ka buɗe “Data Account” ka zaɓi “GPRS” 12. Ka buɗe “Data Account” ka zaɓi, zaɓin ka na shida a sama. 13. Sai gyara ‘account’ ɗin ka kamar haka: APN: MTN: web.gprs.mtnnigeria.net GLO: wap.gloworld.com AIRTEL: wap.ng . airtel.com ETISALAT: wap.etisalat.com.ng 14. Wajen “Username” sai ka rubuta “ wap. Password: shima ka rubuta wap. Kana kammala wa sai ka fito da ga wajen. Ina mai tabbatar maka cewa kana yin haka to wayarka ƙirar China ka za ta fara aiki wato browsing. Idan ka gwada ya yi to sai ka samma abokai da suke da irin waɗannan wayoyin kuma suna sha’awar su shiga wannan tsarin, amma basu san yadda ake yi ba.

Snack's 1967